Isra’ila Na Ci Gaba Da Kai Hare hare Gaza

IDF ta kai sabbin hare-hare a Gaza
Hayayi ya turnike sararin samaniyar Gaza

Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare hare a Zirin duk da matsayar da shugaba Donald Trump ya ce an cimma game da shirin kwance makamai da kungiyar Hamas ta sanar da amincewa da shi.

Bayanai sun ce rundunar sojin IDF ta kai sabbin hare-hare a Gaza, inda ta kashe akalla mutane biyu a cikin awanni 24 da suka gabata, wanda ya sanya har yanzu akai zaman dar-dar a yankin.

A makon ne Donald Trump da Hamas suka ambaci yarjejeniyar da za ta kawo karshen fadan, wacce ta ba da damar janye sojojin Isra’ila a hankali, da kuma kwance damarar makamai daga kungiyar ta Hamas.

Amma Isra’ila har yanzu ba ta amince da yarjejeniyar a hukumance ba.

Duk da cewa Benjamin Netanyahu ya ki cewa uffan, Ministan Tsaron Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, ya bayyana kin amincewa da yarjejeniyar, yana mai cewa “ba za a yarda da ita ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted