Al-Houthi: ‘Isra’ila’ da Amurka na son raba yankin Gabas ta Tsakiya don fadada ikonsu

Shugaban kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik al-Houthi ya jaddada cewa tsawon shekaru kasar Siriya ta taka muhimmiyar rawa wajen bijirewa manufofin Isra’ila.

Shugaban kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik al-Houthi ya jaddada cewa tsawon shekaru kasar Siriya ta taka muhimmiyar rawa wajen bijirewa manufofin Isra’ila.

Sayyed al-Houthi ya yi kira da a hada kai da Syria da al’ummarta, yana mai yin Allah wadai da cin zarafi da kuma keta hurumin kasar Syria da Isra’ila ke ci gaba da yi, da kuma yin amfani da yake-yaken da take yi domin karfafa tasirinta a yankin.

Ya yi ishara da kalaman baya-bayan nan da jami’an Isra’ila, musamman firaministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya bayyana faduwar gwamnatin Syria a matsayin wata babbar dama ga Isra’ila domin sake shata iyakokinta.

Sayyed al-Houthi ya yi gargadin cewa shirin mamaya na Isra’ila zai wargaza yarjejeniyoyin da aka cimmawa kan batun iyakoki, da kuma yin amfani da faduwar gwamnatin Syria wajen fadada mayarta a cikin kasashen larabawa.

Isra’ila na kallon abubuwan da ke faruwa a kasar Siriya a halin yanzu a matsayin wata dama domin cin karenta babu babbaka a cikin Syria da yankin gabas ta tsakiya, ya kuma kara da cewa yana cikin manufofin haramtacciyar kasar Isra’ila na neman wargaza yankin gabas ta tsakiya ta hanyar aiwatar da shirtin rarraba kasashe masu rauni da kuma tabbatar da ikonta a cikinsu, kamar yadda yake faruwa yanzua  Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments