Ma’aikatan lafiya sun shaida cewa an kai gawawwakin mutum bakwai Asibitin Al-Awda da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza, bayan Isra’ila ta yi luguden wuta a wani gida na iyalan Abu Owemer.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta a yankin Shejaiya da ke gabashin Birnin Gaza, inda suka lalata gidaje da dama, kamar yadda wata majiya ta gaya wa Anadolu.
Kazalika wata majiya a Asibitin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza, ta ce Isra’ila ta kashe mutum guda sannan ta jikkata da dama a hare-hare ta sama da jiragenta suka kai yankin Bani Suhaila na gabashin Khan Younis.
Haka kuma Isra’ila ta kashe wani mutum guda a Rafah a yayin da yake taimaka wa motocin da ke ɗauke da kayan agaji da ke wucewa ta yankin, in ji majiyoyin da ke asibitin yankin.
Da ma dai Isra’ila ta daɗe tana kai hari kan ma’aikatan da ke taimaka wa motocin kayan agaji da ‘yan sanda, inda ta kashe gommai.