Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ya bayyana cewa; Kasarsa za ta ci gaba da mu’amala ta kasuwanci da jamhuriyar musulunci ta Iran a karkashin dokokin kasa da kasa, kuma Islamabad ba za ta yi aiki da takunkunmin da aka kakaba ta gefe daya ba.
A yau Alhamis ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan Tahir Andarabi wanda ya gabatar da taron manema labaru a birnin Islamabad ya bayyana cewa; kakaba takunkumi na kashin kai kuma daga gefe daya, yana tattare da matsaloli masu yawa, wanda Pakistan ba za ta yi aiki da shi ba.
Haka nan kuma ya ce; Pakistan tana son ci gaba da kasuwanci da Iran kamar yadda kasashen biyu suke da yarjejeniya akai.
Dangane da halin da ake ciki a mashigar Ruwan Hurmuz kuwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Pakistan ya bayyana yadda kasashen yankin suke kokarin ganin an warware wannan matsala tare da nuna fatan ganin cewa ba da jimawa ba za a sami mafita.
Akan ziyarar bayan nan da babban hafsan sojan Pakitsan ya kawo zuwa Iran, ya bayyana cewa; Fildi Mashal ( Field Marshal) Asim Munir ya gudanar da tattaunawa mai muhimmanci tare da jami’an jamhuriyar musulunci.” Haka nan kuma ya ce; ziyarar tana nuni ne da girman karfin tsayin Islamabad akan matsayarta na lalubo hanyoyin warware rikicin wannan yankin.