IRGC Sun Kama Jiragen Ruwa Biyu Da Su Ka Saba Dokar Wucewa Ta Mashigar Ruwan Hurmuz

 Dakarun kare Juyin musulunci na Iran ( IRGC) sun sanar da kame jiragen ruwa biyu da suke kokarin wucewa ta mashigar ruwan Hurmuz ba tare

Iran ta yi gargadin kai hari kan duk jirgin sojin da ya yi yunkurin shiga Hormuz

 Dakarun kare Juyin musulunci na Iran ( IRGC) sun sanar da kame jiragen ruwa biyu da suke kokarin wucewa ta mashigar ruwan Hurmuz ba tare da bin sabbin ka’idoji ba.

Sanarwar da dakarun kare juyin musuluncin na ta ce da safiyar Larabar nan ne dai su ka tsayar da jiragen ruwan biyu masu sunan; ” MSC-FRANCESCA’ da kuma “EPAMINODES”, daya mai alaka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila, dayan kuma saboda keta doka.

Tuni dai dakarun kare juyin juya halin musuluncin su ka tasa keyar jiragen ruwan biyu zuwa wata tashar jiragen ruwan Iran domin gudanar da bincike.

Iran ta sha nanata cewa, duk wani jirgin ruwa wanda zai wuce ta wannan yankin ba tare da izini ba, to zai fuskanci mayar da martani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted