Search
Close this search box.

IRGC : Isra’ila Za Ta Fuskanci Babban Martani Daga ‘Yan Gwagwarmaya

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya ce Isra’ila za ta fuskanci “mummunan martani daga bangaren ‘yan gwagwarmaya” kan ayyukan

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya ce Isra’ila za ta fuskanci “mummunan martani daga bangaren ‘yan gwagwarmaya” kan ayyukan ta’addancin da ta ke yi a kasar Labanon.

A wata wasika da ya aikewa shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah a jiya Alhamis, Manjo Janar Hossein Salami ya yi Allah wadai da ta’addanci na gwamnatin mamaya, wanda ya yi sanadin shahada da raunata dimbin ‘yan kasar Lebanon da mayakan Hizbullah”.

“Ina shelanta cewa irin wadannan ayyukan ta’addanci, wadanda babu shakka sun samo asali ne sakamakon yanke kauna da gazawar gwamnatin Sahayoniya.

Janar Salami ya yabawa mayakan Hizbullah da kuma al’ummar kasar Labanon bisa goyon bayan da suke baiwa Falasdinawa a yakin da suke yi da mamayar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments