Sanarwar da dakarun kare juyin musuluncin su ka fitar, ta kunshi cewa; Makiya sun kawo hari a kasarmu da safiyar yau Litinin ta hanyar amfani da makamai masu linzami samfurin “Ballastic”.
A gefe daya wani kwararre akan harkokin tsaro dan kasar Iran Mukhtar Haddad ya ce; Da sani da kuma hadin bakin Amurka Haramtacciyyar kasar Isra’ila ta kawo wa Iran hari.
Mukhtar Haddad ya kara da cewa; Hare-haren da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kawo wa Tehran da sauran biranen Iran da su ka hada Tabriz, Isfahan da Karaj, wuce gona da iri ne mai hatsari,wanda zai kawo karshen duk wani batun tattaunawa da kuma shiga tsakani da ake yi.
Haka nan kuma ya ce; Dakarun Iran sun kara shirya kansu a cikin lokacin tsagaita wuta,don haka za su kai wa Tel Aviv hae-hare masu zafi.
Har ila yau y ace; Wannan yakin da aka bude, zai shafi dukkanin wannan yankin ya kuma tsallake shi,kamar yadda shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran ya sanar.
Bugu da kari Haddad ya ce martanin da Iran din za ta mayar ba zai takaita akan Haramtacciyar kasar Isra’ila ba, zai shafi manufofin Amurka idan har ta shiga ciki kai tsaye.