Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Makiya za su biya mummunan farashi ta fuskar tattalin arziki da kuma ta soja, sakamakon harin da suka kai kan Tsibirin Larak
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), Birgediya Janar Hossein Mohebi, ya yi ikirarin cewa: Tabbas maƙiya ‘yan ta’adda zasu biya farashi ta tattalin arziki da ta soja sakamakon harin da suka kai kan Tsibirin Larak da ke kudancin Iran.
A wani rubutu da aka wallafa a shafin yanar gizo a dandalin X a daren Lahadi, Birgediya Janar Mohebi ya jaddada cewa: “Wannan matakin babban kuskure ne na dabarun gwamnatin Donald Trump a lokacin yakin tattalin arziki; kuskure ne da zai canza daidaiton iko a kan masu aikata laifuka tare da haifar musu da hasara mai yawa.”
Ya kara da cewa: “Makiya za su biya mummunan farashin saboda wannan kuskuren lissafi a bangarorin tattalin arziki da na soja.”