Ma’aikatar noma da kiwo ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa kasar ta kai matsayin wadata da abinci musamman a bangaren naman kaji, saboda a halin yanzu tana samar da tone miliyon biyu na naman kaji a ko wace shekara. Alhali tana bukatar tone miliyon 1.6 ne kadai.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar tana cewa, Iran kasashe mai mutane fiye da miliyon 90 abin al-fakhari ne ta sami wadata a bangaren naman kaji don shi ne mafi yawan mutanen kasar suke ci, idan an kwatanta da jan nama na shanu da rago wadanda suka fi tsada.
Kaza dai yana daga cikin abincin mafi yawan Iraniyawa, don haka wadatuwa da shi, wani abu mai muhimmanci ne, musamman a lokacin makiya suka dora mata takunkuman tattalin arziki ko ta ina.
Ma’aikatar ta kammala da cewa a halin yanzu Iran tana da cibiyoyin samar da kaji ya bunkasa da kasha 5% a cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma samar da su kama da samar da kwai, da kenkeshesu, da samar da abincin su, da wuraren kiwonsu, da yankasu, da kuma sarrafasu da kuma rarrabasu zuwa ko ina a kasar suna tafiya kamar yansa aka tsara.