An Sami Dawowar Kwanciyar Hankali A Birnin Yamai Bayan Wani Bore Na Sojoji

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Nijar sun ce an sami dawowar kwanciyar hankali a babban birnin kasar Yamai bayan da wasu sojoji su ka
Shugaba Thiani

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Nijar sun ce an sami dawowar kwanciyar hankali a babban birnin kasar Yamai bayan da wasu sojoji su ka yi bore a ranar Asabar  tare da yin fada a tsakaninsu da sojojin da suke kare gwamnati.

Fadan na ranar Asabar dai ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama da kuma jikkata wasu, a lokacin da sojojin masu bore su ka yi kokarin kutsawa cikin fadar shugaban kasa.

 Kafar watsa labaru ta “Africa News” ta ce sojojin da su ka yi bore suna nuna rashin jin dadinsu ne akan gajiyawar gwamnati na murkushe masu tsattsauran ra’ayi dake dauke da makamai.

A cikin wannan shekarar, wannan shi ne karo na uku da aka yi fada irin wannan, sai dai biyu na bayan suna da alaka ne da masu jabun jihadi dake da alaka da alka’ida da kuma kungiyar ISWAP.

Wani mazaunin birnin Yamai ya fada wa kafar watsa labarun ta “Africanews” cewa; Da Zarar ka ji cewa sojoji sun yi bore, to da akwai wani abu a kasa.”

Hassan Assoumana ya kuma kara da cewa:

“Abinda ya faru, yana nufin cewa sojojin suna da wata bukata,don haka ya zama wajibi ga masu Mulki da su saurare su domin lalubo mafita. Rasha wacce take da sojoji a kasar ta Nijar ta bayyana cewa, sojojin nata sun taka rawa wajen murkushe sojojin da su ka yi bore.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted