Sheikh Qasim: Jajircewar Mutanen Lebanon Ya HKI Rauni

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a wani Jawabin da ya gabatar a taron hadin kan musulmi

Sheik Naeem Qasim babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa jajircewa da hakurin masu gwagwarmaya a yankin yammacin Asia kama daga dakaru kungiyar Hizbullah da mutanen kudancin kasar ko sauran masu gwagwarmaya a Iran da Yemen da Iraki, su suka sa HKI ta yi rauni kuma yasa muke fatan nan gaba zamu dawo da matsayimmu da yankunammu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a wani Jawabin da ya gabatar a taron hadin kan musulmi wanda aka gudanar a nan Tehran ta kafar hotunan bidiyo a jiya Lahadi.

Sheikh Qasim ya kara da cewa, duk da cewa akwai rasa rayuka da kuma asarori masu yawa a wannan jajircewar, amma ya cancanci hakan, saboda makomarmu da yayammu yana tare da jajircewar da mutanen yankin suke yi .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted