Iran: Nakiyoyi Sun Rusa Katafaren Jirgin Dakon Mai A Hurmuz

Majiyar dakarun Juyin juya halin musulunci na kasar Iran ta bada labarin cewa, wani katafaren jirgin ruwan dakon danyen man fetur ta yi kokarin satar

Hoton jiragen ruwa

Majiyar dakarun Juyin juya halin musulunci na kasar Iran ta bada labarin cewa, wani katafaren jirgin ruwan dakon danyen man fetur ta yi kokarin satar hanya a matsagar ruwa ta Hurmuz amma sai da gamu da manya manyan nakiyoyi guda biyu wadanda suka sa ya kama da wuta sannan hakan ya tilasta masa tsayawa cik a inda yake.

Labarin ya kara da cewa jirgin ruwan ya yi kokarin satar hanya, wato ta inda hukumar kula da zirga zirgan jiragen ruwa ta mashigar ruwa ta hurmur bata amince ba a lokacinda ta fada cikin wannan musibar.

Ya kara da cewa wannan shi ne makomar duk wani jirgin da ya yi kokarin satar hanya a mashigar ba tare da izini da kuma bin hanyar da hukumar ta amince da shi ba.

Gwamnatin JMI ta rufe mashigar ruwan ta Hurmuz ne bayan da Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki da nufin kifar da gwamnatin kasar da kuma wargaza kasar Iran a ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekara ta 2026.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted