Cibiyar kare hakkin bil’adama ta “Mirsad” ta bayyana cewa; sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa cikin yankin Tuddan “Durai’at”wanda yake a yammacin kauyen al’muallakha da kusa da gundunar Kunaidara ta kudu.
Cibiyar kare hakkin bil’adaman ta kasar Syria ta kuma ce, sojojin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun yi amfani da tankokin yaki biyu a yayin kutsen nasu, sai dai kuma sun fice daga baya.
Tuddan “Dura’iat” da sojojin mamayar su ka kutsa yana cikin cibiyoyin da sojojin Syria suke amfani da su a baya, wanda kuma yake a matsayin layin tsagaita wuta a yakin 1974 tsakanin Syria da kuma Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
A cikin watan Ogusta ma dai sojojin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kutsa cikin wannan yankin da tankokin yaki biyu.
Haramtacciyar Kasar Isra’ila dai ta mayar da kutse cikin Syria aikin kowace rana, tun bayan faduwar gwamantin Basshar Assad a ranar 8 ga watan Disamba na 2024.