Iran Mutane 2 Su Ka Yi Shahada Sanadiyyar Harin Ta’addancin Amurka A Tsibirin “Lark”

Gwamnan gundumar yankin Qashm ne ya sanar da shahadar mutane 2 da jikkatar wasu da dama saboda harin da Amurka ta kai wa tsibirin "Larka"
Gawawwakin Shahidan Lark

 Gwamnan gundumar yankin Qashm ne ya sanar da shahadar mutane 2 da jikkatar wasu da dama saboda harin da Amurka ta kai wa tsibirin “Lark” a jiya Lahadi da dare.

Gwamnan gundumar ta tsibirin Qashm Hussain Amir Taimur ya  kuma ci gaba da cewa; mutanen da su ka jikkata sanadiyyar harin ta’addancin na Amurka suna karbar magani a asibitin yankin.

Da safiyar yau Litinin ne dai dakarun kare juyin musulunci na Iran su ka sanar da cewa sun mayar da martani akan sansanonin Amurka da suke a kasar Jordan da kuma a UAE.

Sanardar da IRGC ta fitar ya kunshi cewa; Dakarun kare sararin samaniya na IRGC sun kai harin gargadi da jan kunne akan cibiyar sojan Amurka na sama dake cibiyar sarki Hussain da kuma Arzaq. An kuwa kai harin ne da bayar da taken “Ya Muhammad Bin Abdullah s.a.w”.

Dakarun kare juyin musuluncin na Iran sun kuma ce, sun yi amfani ne da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki wajen russa muhimmanci wurare da gine-ginen cibiyar jiragen saman Amurka.

Haka nan kuma sanarwar ta ce a sanadiyyar kai wadannan hare-haren an rusa cibiyoyin na sojojin Amurka.

Haka nan kuma IRGC sun sanar da cewa, hare-haren na sojojin Amurka ba za su raunana karfin Iran na rufe mashigar Ruwan Hurmuz ba, kuma kowane hari da makiya za su kawo wa Iran, za su fuskanci mayar da martani mai tsanani ga abokan gaba. Tsibirin “Lark” yana daga cikin yankunan gundumar Qashm a gabar Ruwan tekun Pasha a kudancin Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted