Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kai hare hare kan sansanin sojojin kasar a kasar Jordan a safiyar yau Litinin bayan da suka kai hare hare kan tsibirin Larak da ke cikin tekun Farisa.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar IRGC na cewa sun yi amfani da makamai masu linzami da kuma Drones wajen maida martani a kan sansanin sojojin Amurka na Sarki Hussain da kuma na Al-Azraq a kasar ta Jordan.
Sun ce makaman sun lalata gine gine dauke da jiragen yakin Amurka da kuma wuraren gyaransa da kuma wasu wurare masu muhimmanci a sansanonin a daren Lahadi 30 ga watan Augusta na shekara ta 2026.
Bayanin ya kara da cewa, hare haren Amurka a tsibirin Laeak ba zai taba warware matsalolin da take fuskanta saboda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz ba.
A wani labarin kuma bayan hare haren da jiragen Amurka suka kai kan tsibiran Larak na kasar Iran, inda daga nan ne Iran take fidda mafi yawan danyen man kasar zuwa kasuwannin duniya, sun tura jirgin leken Asiri da kuma kai hare hare samfurin MQ-9 wanda nan da nan dakarun suka kakkabo shi.