Shugaban Kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan Ya Ce: Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Kowane Hari Da Aka Kai Ma Ta

Shugaban kasar Iran ya bayyana haka ne gabanin tafiyarsa zuwa kasar Kyrgyzstan domin halartar taron kungiyar Shanghai (SCO).

Shugaban kasar Iran ya bayyana haka ne gabanin tafiyarsa zuwa kasar Kyrgyzstan domin halartar taron kungiyar Shanghai (SCO).

Shugaba Mas’ud Pezeshkiyan ya ce; Mu ba ‘yan inda da yaki ne ba, kuma wannan shi  ne sakon da muke aikewa duniya. Sai dai kuma ba za mu taba zama zura idanu mu zama ‘yan kallo ba a gaban duk wani hari da za a kawo mana.”

Shugaban kasar ta Iran ya kuma yi kira ga kasashen yammacin Asiya da su hada karfi  wuri daya domin tabbatar da tsaro da ci gaba na tattalin arzikin yankin.

Shugaba Mas’ud Pezeshkiyan ya kuma yi Ishara da muhimmacin taron SCO domin ya hada shugabannin kasashe da dama wuri daya a lokacin da wasu cibiyoyi suke kokarin mayar da kansu ‘yan sandan duniya.

Haka nan kuma shugaban kasar na Iran ya yi fatan ganin taron na Kyrgyzstan da kuma ganawar bayan fage da za a yi a tsakanin shugabannin kasashe za su taimaka wajen samar da yanayi mai inganci a fagen tsaro da tattalin arziki a cikin wannan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted