Modi: Indiya A Shirye Take Ta Fadada Kasuwancinta Da Iran

Fira Ministan kasar Indiya Narendra Modi ya jaddada cewa kasarsa za ta fadada tsohuwar alakar da take da ita da Iran musamman a fagen kasuwanci.
Fira ministan Indiya Da Shugaban Kasar Iran

Fira Ministan kasar Indiya Narendra Modi ya jaddada cewa kasarsa za ta fadada tsohuwar alakar da take da ita da Iran musamman a fagen kasuwanci.

Modi ya wallafa wannan sakon ne a shafinsa na X bayan ganawar da ya  yi da shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan a bayan fagen taron kunsgiyar Shanghai ( SCO) wanda aka yi a birnin Bishkek na kasar Kyrkgyzstan a yau Litinin.

Shugaban kasar ta Iran da kuma Fira Ministan kasar ta Indiya sun tattanawa akan halin da ake ciki a wannan yankin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Indiya Randhir Jaiswal ya bayayna tattaunawa da shugabannin kasashen biyu su ka yi da cewa ta haifar da Da, mai ido.”

Haka nan kuma ya ce, bangarorin biyu sun tattauna akan alakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a wannan yankin.

Jaiswal ya kuma kara da cewa; a yayin wannan ganawar a tsakanin Modi da Pezeshkiyan fira ministan na Indiya ya jaddada muhimmanci warare sabanin da ake da shi ta hanyar tattaunawa.

A gefe daya an yi wata ganawar a tsakanin shugaban kasar ta Iran da kuma takwaransa na Tajikistan Imam Ali Rahman, inda dukkaninsu su ka jaddada muhimmancin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.

Bangarorin biyu sun bijiro da yadda alaka take a tsakanin Tahran da Doshanbeh da kuma bunkasa abubuwan da su ka yi tarayya akansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted