Sojojin kasar Iran sun bada labarin kai hare hare kan sansanin sojojin AL-Minhad na jiragen sama mallakin Amurka a kasar UAE kusa da birnin Dubai.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin na cewa sun yi amfani da makaman Kamikaze Drones don maida martani kan sojojin Amurka a yankin.
Labarin ya kara da cewa makaman sun fada kan gine ginen da aka ajiye jiragen yaki masu saukar Ungulu na Amurka wadanda suke tazarar kilomita 24 daga birnin Dubai na HDL.
Labarin ya kammala da cewa hare haren maida martani ne kan hare haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan tsibirin Larak cibiyar fitar da danyen man Iran zuwa kasuwannin duniya a cikin tekun farisa.
Hare haren dai sun kashe dakarun IRGC da dama da kuma fararen hula wadanda basu san hawa ko sauka ba.
Sojojiun sun bayyana cewa zasu ci gaba da nuna turjiya don kare kasarsu har zuwa lokacinda makiya zasu tabbatara da hannkinsu.
Daga karshe sojojin su n bayyana cewa an sanyawa farmakin suna Muhammadu Rasulullah.(a) don neman albarkansa.