Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun bayyana cewa; Tabbas daukar fansar Isma’ila Haniyyah yana nan tafe, kuma makircin kwance damarar yakin kungiyar Hamas ya ci tura.
Sanarwar da dakarun kare juyin musulunci su ka fitar ta zo ne adaidai lokacin da ake cika shekaru biyu da shahadar shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyyah a nan Iran da ‘yan sahayoniya su ka yi.
Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa; Daukar fansar jinin shahidi kuma jagora na juyin musulunci da kuma Isma’ila Haniyyah, wani abu ne da ya zama wajibi, kuma martanin na Iran zai zama mai tsananin gaske.”
Bugu da kari sanawar ta IRGC ta yi Magana akan makircin kwance damarar yakin kungiyar Hamas tana mai cewa, babu wani sakamako da za a samu akan hakan, domin Shirin ya riga ya rushe.”
Dakarun kare juyin musuluncin na Iran sun ce “Daukaka da izza gwagwarmayar fada da ‘yan sahayoniya wani abu ne da ba za a taba dankwafe ta ba, kuma al’ummar falasdinu ce za ta sami nasara ta karshe akan ‘yan sahayoniya.”
Bayanin ya kuma ce; Kisan gillar da ‘yan sahayoniya su ka yi wa Isma’ila Haniyyah a lokacin da yake bakunta a Iran domin halartar rantsar da shugaban kasa,babban laifi ne da kuma keta dokokin kasa da kasa.
A ranar 31 ga watan Yuli na 2024 ne dai Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa Isma’ila Haniyyah kisan gilla a masaukinsa dake birnin Tehran, a lokacin da zo halartar taron rantsar da shugaba Mas’ud Pezishkiyan.