Jagoran Juyin Juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa zirin Gaza ne damuwar duniya ta farko a yau.
A yau, Gaza ita ce babban kalubalen duniya; Gwamnatin Isra’ila da magoya bayanta na Amurka da na Turai ba za su iya kawar da batun Gaza daga ajandar ra’ayin al’ummar duniya ba;
Dubi jami’o’in Amurka da na Turai! Dole ne a ci gaba da matsin lamba sosai kan gwamnatin Isra’ila.
Kada mu bari wannan batu ya bace daga ra’ayin jama’a na duniya.
Halin da Amurkawa ke nunawa a lamarin Gaza ya tabbatar da ingancin matsayin Iran na rashin amincewa da Amurka.
Dole ne Falasdinu ta koma ga masu mallakarta na asali.
A hannu guda kuma jagoran ya bayyana cewa ‘’Daidaita dangantaka da gwamnatin Isra’ila ba zai taba magance matsalar yammacin Asiya ba.
Jagoran ya bayyana haken ne a lokacin da yake ganawa da wani rukunin malamai a dalilin zagayowar ranar malamai ta kasa a Iran.
Muhimman batutuwan da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi a yayin wannan ganawa su ne ;
Jinjinawa malamai da karfafa masu guiwa akan bada ilimi mai nagarta da amfani ga bil adama.
Jagoran ya kuma bayyana cewa : ‘’Ya kamata matasa su san ma’anar da ke bayan taken “kin jinin Amurka” da mulkin mallaka da salon mamaya na gwamnatin Isra’ila.”