Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa JMI zata maida martani kan duk wata kasa wacce ta bawa HKI damar amfani da kasar don kaiwa kasarsa hari.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Qalibof yana fadar haka a hari ta musamman da shi a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Asabar.
Ya kuma kara da cewa ya na fatan kasashen da suke makobtaka da kasar Iran za su dauki wannan al-amarin da muhimmanci, kamar yadda yake a baya.
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya ce Iran tana da kekyawar dangantaka da kasashen da suke makobtaka da ita, don haka ba ya zaton hakan zai faru.
Qolibof ya kara da cewa: Kasar Iran ba ta son yaki kuma ba ta bukatar a fadada yakin da ke faruwa a Gaza zuwa sauran kasashen yankin. Ammam idan an tilastamata shiga yakin to kuma zata maida martani da karfin gaske ne.
A ranar daya da watan Octoban da muke ciki ne dakarun IRGC na kasar Iran suka maida martani kan HKI da makamai masu linzami har 200 bayan kissan Isma’il Haniya shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinawa, da kuma Sayyid Hassan Nasarallah shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon. Hare-haren ‘wa’adus Sadik na II sun nuna irin karfin da makaman Iran suke da shi.