Ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta maida martani ga bukatar Amurka na komawa kan teburin tattaunwa da kuma sulhu don kawo karshen yakin da ta farwa kasar Iran da shi a farkon wannan shekarar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Gujiyo koon, ya bayyana haka ne a safiyar yau litinin, a lokacinda yake jawabi ga kafafen yada labarai, ya kuma kara da cewa yakin baya amfanar kasashen biyu, kuma yana cutar da kasashen yankin da makasashen duniya da dama.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China ya kara da cewa, babu wata mafita don kawo karshen wannan yakin sai komawa kan teburin tattaunawa.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka yar ta’adda, Donal Trump ya bayyanawa tashar talabijin ta CBS kan cewa yakin da ya fara a kasar Iran ya kuma kasa kammala shi a cikin lokaci, tsadar farashin man fetur da kuma kiyayyar HKI ne suka kada Jam’iyyarsa ta Republican a zaben makon da ya gabata.
Sannan ya kara da cewa, kasashen da ya shiga yaki don karesu ne zasu biya dukkan barnan da aka yiwa kasarsa a wannan yakin. Saboda ba don taimakon Amurka ba da babu su a yankin.