Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran ta gabatar da shirin bude mashigar ruwa ta Hurmuz na tsawon kwanaki biyu kacal, don nuna tausayi da wasu kasashen da abin ya shafa don kama dawo da zaman lafiya a yankin da sauri.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esma’il Baghaei kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka a safiyar yau litinin ya kuma kara da cewa, wannan damar tana nan ga Washington idan tana bukatar warware wannan matsalar. Yace wannan duk bayan da Amurka ta cika sharuddan kasar ne hakan zai faru.
Wannan yana zuwa ne bayan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana sharuddan kasar Iran a matsayin masu tsauri, masu bammamaki wasun kama ba zasu taba yiyuwa ba.
Baghaei ya mayarwa Rubio da amsa kan cewa babu abin mamaki ko kuma wanda ba zai taba yiyuwa ba a sharuddan kasar Iran, na neman hakkinta a matsayin kasa mai cikekken yencin kanta.
Sai ya tambaya, yana cewa :menene ba zai yu ba a cikin sharuddan, hakkimmu da muke son a mayarmana ne, kuma menene wanda babu hankali a cikinsa?. Tehran ta bukaci a kawo karshen yaki a dukkan wuraren da ake yaki da ita da kawayenta, wannan ba zai yu ba? Ko kuma dauke mana daukunkuman da aka dora mana don kifar da gwamnatin kasarmu? Kuma wannene ba zai taba yiyuwa ba? Yace duk bukatun kasar Iran, suna kan hanya, hakkinta ne kuma basu kaucewa hanya ba, kuma duk masu yiyuwa ne.
Daga karshen ya ce, idan wani ko Amurka tana da wani shiri wanda yafi wanda muka gabatar zama mai adalci ya kawo.