Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya, da hare-haren da aka kai wa kayayyakin more rayuwa na fararen hula da yankunan da fararen hula ke zaune a Yemen.
A cikin wata sanarwa ma’aikatar ta sake nanata “Matsayin Iran na Allah wadai da duk wani keta ‘yancin kasar Yemen.
Ma’aikatar ta jaddada cewa “ci gaba da kai hare-haren kan ‘yancin kasar da kuma toshewar tattalin arziki da aka sanya wa kasar, sun saba wa dokokin kasa da kasa.”
Harin baya bayan nan shi ne wanda aka kai a ranar 6 ga Nuwamba a kasuwar Al-Hadara da ke gundumar Al-Wazi’iyah ta Jihar Taiz, wanda ya kashe fararen hula ‘yan Yemen 33, ciki har da yara 13, tare da raunata wasu da dama.”
Ma’aikatar ta kuma yi Allah wadai da “harin jiragen sama da aka kai a kauyen Al-Shariya a gundumar Bani Hushaysh, gabashin Gundumar Sana’a, wanda ya kashe mutane 33, ciki har da mata da yara da dama, da kuma hare-haren da aka kai wa ma’aikatan gidan talabijin na Al-Masirah yayin da suke gudanar da aikinsu na jarida.”
A cewar sanarwar, “wadannan hare-haren ba wai kawai sun saba wa Mataki na 2, sakin layi na 4 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ba ne, har ma sun saba wa dokokin jin kai na duniya kuma sun zama laifukan yaki.”
Iran ta jaddada cewa “rikicin da ke tsakanin Saudiyya da Yemen dole ne a warware shi wuri-wuri ta hanyar tattaunawa tsakanin bangarorin.