Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran sun baje kolin irin ci gaban da ta samu a fagen kere-keren makamai wadanda suka hada da jiragen yakin Drons, wadanda ake sarrafasu daga nesa, da ko UAVs da makamai masu linzami daban daban, da kuma ayyukansu a fagen sararin samaniya, wadanda suka hada da Lombo mai daukar taurarin yan’adam zuwa falakansu a sararin samaniya.
Tashar talabijin ta Presstv ta bayyana cewa dakarun sun baje kolin kayakin ne na wurin baje kolin irin wannan kayakin da ke nan birnin Tehran. Wato Wurin baje kolin kayakin sararin samaniya ta kasa ” National Aerospace Park’.
Kafin haka dakarun sun bude wani bajekolin amma na ci gaban da ta samu a shirinta na makamashin nuklia na zaman lafiya a wurin da ta saba yin yin haka a garin ray na kudancin kasar ko kuma kusa da haramin Sha Abdul-Azim Al-Hassani dake kudancin birnin Tehran.
An bude kasuwar baje kolin kayakin da aka samar daga makamashin nukliya a zauren Sheikh Kulayni daga ranar 7-11 ga watan Nuwamba daga karfe 10-na safe zuwa 5 na yamma. An baje magunguna, kayakin aikin noma,da Plasma, da wasu na’urorin da suke taimakawa wajen gano cutar kansa da sauransu. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu mutane kimani miliyon biyu a duk fadin kasar suke amfana da wadannan ci gaba a cibiyoyi 253 da aka bude a duk fadin kasar.