Aragchi: Mutanen Asia Da Amurkawa Sun Kosa Da HKI

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, mutanen a kasashen yammacin Asiya da kuma Amurka a baya bayan nan sun nuna cewa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, mutanen a kasashen yammacin Asiya da kuma Amurka a baya bayan nan sun nuna cewa sun kosa da samuwar HKI a yankin yammacin Asia.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a shafinsa na X a safiyar yau litinin, ya kuma kara da cewa, tun fiye da shekaru kimani 80 da suka gabata kasashen yamma musamman Amurka suke goyon bayan samuwar HKI a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, wanda hakan yake jawo masu yake yaken da basa da karshe. Sannan mutanen Amurka a makon da ya gabata sun kada jam’iyyar Repoblican a zaben majalisun dokokin kasar, don su nuna cewa sun gaji da yakin da shuwagabannin kasar suke goyon bayan shekara da shekaru a baya.

Yace mafi yawan Amurkawa basa cikin nutsuwa kuma sun kosa da yake yaken da HKI take jawowa a karsu, yake yaken da basa karewa, don haka akwai bukatar a kawo karshen tallafin da ake bawa HKI don tabbatar da samuwarta a wannan yankin. Yace haka ma , mu ma mun gaji da ganin HKI a wannan yankin.

Kafin wannan sakon Aragchi ga shugaba Trump, an nakalto shi yana cewa, tsananin kin da Amurkawa sukewa HKI, da yakin da gwamnatinsa da HKI suka farwa kasar Iran da shi, da kuma tashin farashin man fetur suna daga cikin dalilan da suka sa jam’iyyarsa ta repuplican ta fadi a zaben rabin wa’adin da aka gudanar a makon da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted