Iran ta bayyana cewa sabon shirin AMurka wanda ya tanadi toshe hanyoyin jigilar kayayaki ta hanyoyin kasa ba zai wani tasiri ba.
Da yake mayar da martani kan shirin Kakakin Rundinar IRGC Birgediya Janar Hossein Mohebbi, ya ce Amurka ba za ta taba iya toshe tattalin arziki na Iran kamar yadda suke tsammani ba.
Ya kara da cewa: “Idan Amurka ta kuduri aniyar bin wannan hanya, to mu ma mun iya haka, musamman tunda mun dauki matakan da suka dace don kiyaye alakarmu da kasashen makwabta.”
Ya jaddada cewa: “Muna da kyakkyawar alaka da makwabtanmu kuma muna da hanyoyi daban-daban na musayar wadannan bayanai, kuma Amurka ba ta da karfi sosai don toshe su.”
Da yake magana game da sabon shirin wanda aka yi wa lakabi da “Kofar Karfe,” mai magana da yawun IRGC ya ce: “Wannan shirin magana ce kawai, kuma Amurka ba za ta cimma burinta na matsin lamba mai tsanani don kawo rugujewa da lalata tattalin arzikin Iran ba.”
Kwamandan Rundunar Tsaron Amurka (CENTCOM) – wadda Iran ta ayyana a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda – ta sanar a ranar Asabar cewa za a kirkiri sabuwar runduna “don hana Iran amfani da hanyoyin kasa don jigilar makamai da sauran kayayyaki.”
Kwamandan CENTCOM Admiral Brad Cooper ya ce rundunar za ta karfafa toshe tashohin jiragen ruwa na Iran.
Rundunar da ke zaune a Tampa, Florida, za ta yi aiki tare da sauran hukumomin gwamnatin Amurka don hana safarar makamai, fasaha, kayan da aka sanya wa takunkumi, da kuma abin da CENTCOM ta kira hanyoyin samun kudaden shiga ba bisa ka’ida ba a kan iyakokin kasar Iran da Tekun Caspian.