IRGC Ya ce: An Kawo Karshen Sace Hanyar Wucewa Ta Hurmuz

Majiyar dakarun kare juyin juya halin muuslunci a nan Iran IRGC Navy ta bayyana cewa, sun kawo karshen sace sacen hanya don wucewa da bangaren

Majiyar dakarun kare juyin juya halin muuslunci a nan Iran IRGC Navy ta bayyana cewa, sun kawo karshen sace sacen hanya don wucewa da bangaren kudancin mashigar ruwa ta Hurmuz kwata kwata a daren jiya. Kuma daga jiya da dare ba wani jirgin ruwa da ya sami damar wucewa da barauninyar hanya a mashigar.

Kamfanin dillacin labaran Tasnim na kasar Iran ya kara da cewa, dakarun sun toshe dukkan hanyoyin da wasu jiragen ruwa suke sace hanyar wucewa, kuma a halin yanzu ba wanda zai iya sace hanya ko da tare da rakiyar sojojin kasar Amurka ne.

Kafin haka dai Brigadier General Mohammad Reza Naghdi ya bada sanarwan cewa zasu rufe dukkan hanyoyin da wasu suka samar suke kuma wucewa a mashigar ruwan ta Hurmuz idan basu yi karo da nakiya ba. Yace duk za’a rufe su kuma a halin yanzu an rufe su.

A wani labarin kuma dakarun na IRGC sun bada labarin cewa hare haren da Amurka ta kai a wasu yankuna na tsibirin Qishm a daren jiya bai lalata kome ba, kuma babu wanda aka jiwa rauni ko asara ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted