Bayanai daga Afrika ta Kudu na cewa Jam’iyyar (ANC), ta sake fuskanat koma baya a zaben kananan hukumomi da aka gudanar.
Jam’iyyar ta Nelson Mandela mai tarihi ta sake fuskantar koma-baya a zaben, wanda ya tabbatar da raguwar tasirinta a tsakanin masu zabe.
A cewar sakamakon wucin gadi, ANC ta kasance babbar jam’iyyar siyasa a kasar, amma da mafi karanci a tarihi.
Jam’iyyar, wadda ke kan mulki tun bayan karshen mulkin wariyar launin fata, tana kan hanyar faduwa da kusan maki 15 cikin dari idan aka kwatanta da zabukan kananan hukumomi da suka gabata, inda ta rasa kusan kashi daya bisa uku na goyon bayan da ta samu shekaru biyar da suka gabata.
Wannan rushewar ta nuna rashin gamsuwar wani bangare na al’umma da wahalhalun rayuwa na yau da kullun da suka hada da rashin aikin yi mai yawa, matsalolin samun ruwa, katsewar wutar lantarki, gazawar ayyukan gwamnati, da kuma rashin tsaro a birane da dama.
ANC ta dade tana da tasiri a kasar, inda ta sami kusan kashi 70% na kuri’un da ta samu.
Jam’iyyar da ta jagoranci Afirka ta Kudu zuwa karshen mulkin wariyar launin fata da dimokuradiyya a shekarar 1994 a karÆ™ashin shugabancin Nelson Mandela.
Duk da koma bayan da ta samu, jam’iyyar ANC ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko a gaban jam’iyyar Democrat Alliance. Amma rarrabuwar kawuna a fagen siyasar Afirka ta Kudu ya tabbatar da wani sabon lokaci na rashin tabbas ga jam’iyyar da ta mamaye harkokin siyasarkasar tsawon shekaru talatin.