Kungiyar Gwagwarmayar Faladinawa ta Hamas ta tabbatar da cewa ci gaba da toshewa da kuma keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta jin kai da Isra’ila ke yi, ya kara jefa dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a yankin Gaza da aka killace, a cikin mawuyacin hali a daidai lokacin da ake tunkarar hunturu, da ambaliyar ruwa, da kuma lalacewar matsugunansu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta bayyana cewa hunturu a yankin, gami da ambaliyar ruwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da lalacewar gine-gine, ya ta’azara ne sakamakon killacewar da Isra’ila ke wa yankin da kuma keta yarjejeniyar tsagaita wuta.
A cewar Hamas, Isra’ila ta ci gaba da hana shigar da kayayyakin agaji na gaggawa, da ake da matukar bukata a wannan yanayin.
Hamas ta kuma soki rashin daukar matakin da ake kira “Majalisar Zaman Lafiya” da babban daraktan ta, Nikolay Mladenov, suka yi, duk da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi, tana mai jayayya cewa matsayinsu ya amince da wadannan ayyukan yadda ya kamata.
Hamas ta kuma yi kira ga kasashen duniya, da kuma kasashen Larabawa da Musulmi, da su dauki matakin gaggawa don dage shingen, domin tabbatar da isar da kayayyaki masu mahimmanci, da kuma kawo karshen shirun da al’ummar duniya ke yi da rashin daukar mataki a kan wahalhalun da Falasdinawa ke sha a Gaza.
A cewar ofishin gwamnatin Gaza, ambaliyar ruwa ta shafi tantuna 70,000, yayin da kusan mutane 400,000 da aka kora ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwa ta fi shafa.