Rashin Aikin Yi Na Dada Karuwa A Faransa

Bayanin ya ce Faransa ta fuskanci karuwar marasa aikin yi 78,000 a cikin wata guda.

Wani kiyatsi da ofishin Eurostat mai kula da kididiga a tarayyar Turai ya nuna cewa, rashin aikin yi a Faransa ya sake karuwa a tsakanin watan Agusta da Satumba na 2026.

A cewar kiyasin na Eurostat, adadin rashin aikin yi a Faransa ya karu daga kashi 8.3% zuwa kashi 8.5%, a yayin da adadin na rashin aikin yi a yankin Turai ya kasance kashi 6.5%.

Bayanin ya ce Faransa ta fuskanci karuwar marasa aikin yi 78,000 a cikin wata guda.

A watan Satumba na 2026, ofishin Eurostat ya kiyasta adadin marasa aikin yi a Faransa ya kai miliyan 2.732, idan aka kwatanta da miliyan 2.654 a watan Agusta.

Shekara guda da ta gabata, a watan Satumba na 2025, adadin rashin aikin yi ya kai kashi 7.9% wanda ya nuna karuwar maki 0.6 cikin dari.

Bayanin ya ce an fi fuskantar wannan a cikin rukunin wadanda ba su kai shekara 25 ba, adadin rashin aikin yi ya kai kashi 21.9 cikin dari.

A yankin Turai, adadin rashin aikin yi na matasa ya kai kashi 15.4%, wanda ya karu da maki 0.3% idan aka kwatanta da watan Agusta na 2026.

Yawan marasa aikin yi na yankin Turai ya ci gaba da kasancewa a kashi 6.5%, duk da ƙaruwar adadin marasa aikin yi.

A watan Satumba na 2026, yankin Turai yana da marasa aikin yi miliyan 11.555, fiye da na watan Agusta.

A cikin Tarayyar Turai mai kasashe membobi 27, adadin rashin aikin yi ya kasance a kashi 6.2%, wato mutane miliyan 13.773 da basa da aiki. Inda kasha 4.1% a Jamus, kashi 6.3% a Italiya, kashi 8.5% a Faransa, sai kuma kashi 10.3% a Spain.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted