Search
Close this search box.

Iran Za Ta Karbi Bakwancin Zaman Taro Tattaunawar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Asiya

Kasar Iran za ta karbi bakwancin tawagogin diflomasiyya 41 a dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen yankin Asiya Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri

Kasar Iran za ta karbi bakwancin tawagogin diflomasiyya 41 a dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen yankin Asiya

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri Kani ya sanar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta karbi bakwancin taron hadin gwiwar kasashen Asiya na {ACD} da zaman taron zai samu halartar tawagogin diflomasiyya 41.

Baqiri Kani a rubutunsa a shafin yanar gizo a yau Lahadi ya bayyana cewa: Iran tana alfahari da karbar bakwancin zaman taron ministocin kasashe karkashin dandalin tattaunawar Asiya a gobe litinin a birnin Tehran fadar mulkin kasar.

Ya ci gaba da cewa: Wannan taron zai samar da wani dandali na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da kuma nuna sha’awar Asiya ta samun fadada da hada kai.

A yau Lahadi ne aka gudanar da zaman taron masana da manyan manajoji na kasashe mambobin kungiyar domin tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan samun daidaito a matakin karshe kan batun tattaunawar taron ministocin da za a yi gobe litinin.

A taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar ACD karo na 18 da aka yi a watan Satumban shekarar 2023, an bayyana cewa, za a mika ragamar shugabancin kungiyar ga kasar Iran.

Abin lura shi ne cewa, tattaunawar hadin gwiwa ta kasashen Asiya (ACD) kungiya ce ta gwamnatoci da aka kafa a ranar 18 ga Yunin shekara ta 2002 don inganta hadin gwiwar kasashen Asiya a matakin nahiya da kuma taimakawa hadewar kungiyoyi daban-daban kamar ASEAN, kungiyar hadin gwiwar yankin Kudancin Asiya, Majalisar Haɗin kai ta Tekun Pasha da Ƙungiyar Tattalin Arzikin kasashen Eurasia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments