Iran Za Ta Karbi Bakuncin  Taron Kungiyar Tattalin Arziki TA “Eco” A Gobe Litinin

A gobe Litinin ne za a bude taron kungiyar tattalin arziki ta “Eco” a nan birnin Tehran,kamar yadda mataimakin ministan harkokin cikin gida na Iran

A gobe Litinin ne za a bude taron kungiyar tattalin arziki ta “Eco” a nan birnin Tehran,kamar yadda mataimakin ministan harkokin cikin gida na Iran Ali Zaini Wand ya sanar.

Taron dai za a yi shi ne a matakin ministocin harkokin cikin gida domin Shata hanyoyin aiki a tare a tsakaninsu, bayan da aka dauki shekaru 15, ba a gudanar da shi ba.

Ali Zaidani ya kuma yi ishara da cewa taron na wannan karon zai mayar da hankali ne akan hanyoyin bunkasa alaka da kasashen makwabta,musamma bisa la’akari da cewa gundumomin Iran da suke aka iyaka suna da kyakkyawar alaka da kasashen makwabta.

Bugu da kari  taron na kungiyar “Eco” zai yi kokarin kawar da kalubalen da ake fuskata da yake kawo cikas wajen kai da komowa a tsakanin kasashen.

Ita dai kungiyar tattalin arziki ta “Eco’ an kafa ta ne a Tehran a 1985 da kasashen Iran, Pakistan da kuma Turkiya. Sai dai daga wasu kasashen sun zama mambobi da su ka hada Afghanistan, Azerbaijan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, Turkmenistan da Uzbakistan.

Manufar kungiyar dai ita ce bunkasa alakar tattalin arziki, kasuwanci da zuba hannun jari. Kasashen suna son samar da kasuwa ta bai daya a tsakaninsu da kai da komon haja ba tare da tsaiko ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments