Search
Close this search box.

Iran za ta gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yuni

Shugabannin sassa uku na gwamnatin Iran sun amince da ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa cikin gaggawa a kasar,  kwana guda bayan

Shugabannin sassa uku na gwamnatin Iran sun amince da ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa cikin gaggawa a kasar,  kwana guda bayan da aka tabbatar da rasuwar shugaba Ibrahim Raeisi a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi a arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana a yammacin jiya litinin cewa, an amince da ranar 28 ga watan Yuni a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasar Iran a wani taro da ya gudana a ofishin shugaban kasa a birnin Tehran.

Taron ya samu halartar shugaban reshen zartaswa na Iran Mohammad Mokhber, shugaban majalisar dokoki Mohammad Bagher Ghalibaf da shugaban ma’aikatar shari’a Gholam-Hossein Mohseni-Eje’i.

Zaman ya kasance na biyu tsakaninbangarorin uku a cikin sa’o’i kadan daga lokacin rasuwar shugaba Raisi a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a lardin Azarbaijan ta gabas.

Doka ta 131  cikia kundin tsarin mulkin kasar Iran ta bukaci manyan jami’an kasar guda uku da su shirya gudanar da zaben shugaban kasa cikin kwanaki 50 daga ranar da shugaba mai ci ya rasu ko kuma ya gaza tafiyar da shugabancin kasa.

An kuma bayyana jadawalin zaben wanda a karkashinsa za a yi rajista daga 30 ga Mayu zuwa 3 ga watan Yuni yayin da ‘yan takara za su kaddamar da yakin neman zabe na kwanaki 15 daga ranar 12 ga watan Yuni.

Masu aikin ceto sun gano tarkacen jirgin mai saukar ungulu da ke dauke da shugaba Raisi da sanyin safiyar ranar jiya Litinin bayan shafe sa’o’i ana bincike wanda ya hada da kungiyoyi sama da 70.

Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian da wasu manyan jami’an lardin tare da ma’aikatan jirgin da masu tsaron lafiyarsu na daga cikin weadanda hatsarin ya rutsa das u.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments