Search
Close this search box.

Iran : ‘Yan Takara A Zaben Shugaban Kasa Sun Tafka Muhawarar Farko Kan Tattalin Arziki

‘Yan takara shida a zaben shugabancin kasa a Iran sun tafka muhawara ta farko kan tattalin arzikin kasar, gabanin zaben da za a gudanar a

‘Yan takara shida a zaben shugabancin kasa a Iran sun tafka muhawara ta farko kan tattalin arzikin kasar, gabanin zaben da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni sakamakon shahadar Shugaba Ebrahim Raisi da mukarabansa a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu da ya gabata.

Muhawarar ta tsawon sa’o’i hudu da ka watsa kai tsaye a gidoan talabijin na kasar ita ce ta farko a cikin guda biyar da aka tsara ‘yna takaran zasayi a cikin kwanaki 10 da suka rage kafin zaben domin maye gurbin Mirigayi Raisi.

‘Yan takarar sun tattauna kan tsare-tsarensu na tattalin arziki da aiwatar da shirin raya kasa, da dabarun yaki da hauhawar farashin kayayyaki, ayyukan kamfanoni masu zaman kansu da bunkasa samar da kayayyaki, da kara shigar da jama’a a fannin tattalin arziki.

Dukkan su sun yi alkawarin yin bakin kokarinsu wajen ganin sun karya laggon tasirin da takunkuman da aka kakabawa kasar suka haifar kan tattalin arziki.

‘Yan takara shida sun gudanar da yakin neman zabe a makon da ya gabata bayan amincewar da babbar hukumar da ke sa ido kan zaben kasar ta yi, inda suka bayyana tsare-tsare da abubuwan da suka sa gaba don samun tagomashin masu kada kuri’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments