Iran: Tofin Allah Tsine Kan Harin Amurka Ga Masu Bikin Aure

Mataimakiyar Shugaban Kasar Iran ta bayyana cewa: Harin da Amurka ta kai wa wani taron daurin aure a gundumar Sirik laifi ne da ya shafi

Mataimakiyar Shugaban Kasar Iran ta bayyana cewa: Harin da Amurka ta kai wa wani taron daurin aure a gundumar Sirik laifi ne da ya shafi bil’adama

Mataimakiyar Shugaban Kasa kan Harkokin Mata da Iyali a Iran, Zahra Behrouz Azar, ta bayyana harin da aka kai kan wani taron bikin aure a Sirik (kudancin Iran), wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, ciki har da yaro daya, da kuma raunata wasu 50 na daban, yana matsayin muggan laifuka, kamar yadda wata takarda ta kara da cewa: Amurka ta aikata laifukan cin zarafin bil’adama.

Kamfanin dillancin labaran “IRNA” na Iran ya ruwaito cewa: Behrouz Azar ta rubuta a dandalin X: “Makiya Amurka ta hanyar mummunan harin da ta kai wa wani taron aure a Sirik, ya lashe rayukan mutane hudu masu daraja, ciki har da yaro daya, inda ya raunata wasu mutane 50 na daban wadanda ba su aika wani laifi ba.”

Ta jaddada cewa: “Masu bikin daurin aure sun koma masu tafiya gudanar da jana’iza, wanda hakan ke matsayin karin dalilin aikata laifuka a tarihin laifukan cin zarafin bil’adama da Amurka ta aikata,” tana mai jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da kuma wadanda suka yi shahada da kuma mutanen garin Sirik da suke cikin halin bakin ciki mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted