Iran Tace IAEA Ta Amince Da Sabuwar yarjeniya Da Ita

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia. A lokacinda yake jawabin hadin guiwa ta tokwaransa na kasar ta Tunisia.

Kafin haka dai Aragchi ya yada zango a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya gana da Rafael Grossi shugaban hukumar IAEA, suka kuma rattaba hannu kan sabuwar yarjeniya da hukumar, ta yadda hulda tsakaninsu zata kasance bayan hare-haren da HKI da Amurka suka kai wa cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar ta Iran.

A dayan bangaren kuma kasashen turai 3 Jamus Faransa da kuma Ingila, sun ki amincewa da sabuwar yarjeniyar, Aragchi ya ce, abin mamaki ne.

Kasashen uku dai suna kokarin ganin Hukumar ta IAEA ta kara takurawa JMI kan shirinta na Makamashin nukliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted