Rundunar Sojin Iran Ta Bayyan Cikekken Goyon Baya Ga Kasar Qatar

Babban hafsan sojojin kasar Iran ya bayyana goyon bayan sojojin kasar Iran ga kasar Qatar, bayan hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha na kasar a ranar laraba a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar hamas na kasar Falasdinu da ta mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Mousavi yana […]
Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar […]
Qatar Ta Bukaci A Gurfanar Da Netanyahu A Gaban Kuliya Don Fuskantar Adalci

Gwamnatin kasar Qatar ta yi tir da fray ministan HKI Banyamin Natanyahu, kuma ta bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya, saboda hare-haren ta’addanci da kai birnin Doha babban birnin kasar a ranar Laraban da ta gabata . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Firay ministan kasar Qatar yana fadar haka […]
Hamas Ta Ce Hare-Haren Isra’ila A Doha Ba zai Sauya Kome A Gaza Ba

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa hare-haren da HKI ta kai shuwagabannin kungiyar masu tattaunawa a doha a ranar talatan da ta gabata, ba zai sauya kome a abinda kungiyar zata gabatar na sulhu a Gaza ba. Shafin yanar gizo na labarai “Arab News” ya nakalto Fawzi Barhoum yana fadar haka a wani faifen bidiyo da […]
Iran Tace IAEA Ta Amince Da Sabuwar yarjeniya Da Ita

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia. […]
Isra’ila Ta Kai Hari Da Makamai Mazu Linzami A Wasu Yankuna Na Yamen

Kasar yamen itace kasar larabawa daya tilo a kasashen musulmi ta duniya da ta mike ta kalubalanci yakin kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take ci gaba da yi kan yankin falasdinu, da Israila ta kira da yunkurin samar da fadaddiyar Isra’ila. Wani babban jami’in soji na kasar yaman ya fadi cewa za su ladabatar […]
Shugaban Najeriya Ya Bada Da Umarnin Karya Farashin Kayan Abinci

Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Najeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce […]
Iran Tayi Tir Da Harin HKI A Yamen Da Kuma Kashe Yan Jarida

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tayi Allah wadai da harin ta’addanci da hki takai kan ginin ma’aikatar sadarwa guda biyu a kasar Yaman da ya kai ga shahadar wasu yan jaridar guda biyu. Har ila yau tayi tir da hari da isra’ila takai kan muhimman wurare a kasar yamen da yankunan farafen hula ,da haka […]
Ana Gab Da Kulla Yarjejeniyar Iskar Gas Tsakanin Iran Da Kasar Rasha.

Jakadan kasar Iran a Rasha ya bayyana cewa daya daga cikin muhimman alamura da ake gab da cimma yarjejeniya akansa tsakaninsu da kasar Rasha a bangaren makamashi shi ne batun kai iskar gas Iran, wanda tuni aka wuce matakin share fage ana gab da kammalawa Kazim Jalali ya fadi a gefen bikin baje kulin kayayyakin […]
Kasar Ghana Ta yi Tir Da Harin Da Isra’ila Takai A Kasar Qatar

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Ghana tabi sahun kasashen duniya wajen yin All.. wadai da harin da Isra’ila ta kai kan ofishin kungiyar Hamas da ke Doha, da kuma bayanashi a matsayin babban laifi a dokokin kasa da kasa. A wani jawabi mai zafi da Ma’aikatar harkokin wajen kasar Ghana ta fitar ta bayyana harin […]
Araghchi :Yarjejeniya da IAEA zata dore idan ba’a dauki mataki kan Iran ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kan batun dawo da hadin gwiwa, za ta ci gaba da wanzuwa matukar dai ba a dauki wani mataki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, ciki har da yunkurin mayar […]
Sheikh Naeem Qassem: Kasashen Larabawa ma ba su tsira ba daga hare-haren Isra’ila ba

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa idan kasashen Larabawa ba su goyi bayan ‘yan gwagwarmaya ba, to su ma za su fuskantar hare-haren Isra’ila” A jawabinsa babban sakataren kungiyar ta Lebanon ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila da Amurka suna aikata munanan laifuka a zirin Gaza da kuma yammacin […]
Faransa : Mutane 250,000 suka shiga zangar zangar ‘’a Toshe komai’’ inji CGT

Kungiyar kwadago ta CGT a faransa ta ce mutane 250,000 ne suka shiga zanga zangar da ake wa lakabi da ‘’A toshe komai’’ a fadin kasar, ko yake hukumomin kasar sun ce mutum 175,000 ne suka halarci zanga zangar ta jiya Laraba. Rahotannin sun ce a babban birnin kasar an yi arangama a kusa da […]
MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike

Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA, kan “tsarin da zai ba da damar komawa bincike a Iran”. A yayin taron manema labarai a wannan rana, Dujarric ya ce wannan yarjejeniya wani mataki […]
Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci

Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade […]