Iran Tace Amurka Tana Kai Hare Hare Kan Muhimman Al-amuran Rayuwa Na Mutanen Kasar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi allawadai da hare haren da sojojin Amurka suka kai kan madatsun ruwa guda biyu a garin Sirik

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi allawadai da hare haren da sojojin Amurka suka kai kan madatsun ruwa guda biyu a garin Sirik da ke bakin ruwa tekun farisa suka lalata su da nufin jefa mutanen yakin cikin mummunan hali na rashin ruwa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto baghaei yana fadar haka a safiyar yau Alhamis a shafinsa na X ya kuma kara da cewa ruwa yana da muhimmanci a rayuwar mutane kimani 20,000 a cikin kauyuka kimani 10 a yankin. Yace madatsun ruwan guda biyu suna bada ruwa kimani cubic meter murabba’ii 500 ga mutanen yankin a ko wace rana.

Baghaei yace, wannan ba kuskure bane, ko kuma bai zama lazimi a rusa madatsun ruwan ba, sai dai abinda ya tabbata shi ne da gangan Amurka ta yi haka don galabaitar da mutanen yankin. Garin Sirik dai yana cikin lardin Hurmuzghan a bakin ruwan Tekun farisa. Kuma lalata wadannan madatsun ruwa yana daga cikin laifukan yaki a dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted