Jakadan kasar Iran na din din din a MDD da na cibiyoyin majalisar da ke kasashen Turai duk sun yi allawadai da hukumar IAEA wacce ta samar da wata doka ta tilastawa Iran ta bayyana yanayin cibiyoyin nukliyar kasar suke, bayan da Amurka ta yi masu luguden wuta a cikin watan yulin da ya gabata, kuma bayan da Amurka ta kasa sace sinadarin uranium na kasar da ke Esfahan a cikin wannan yakin da suke fafatwa.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana, kasashen Amurka, Burtania, Faransa da kuma Jamus ne suka gabatar da bukatar a wani taro na musmman a cibiyar hukumar da ke Geneva inda aka tashi da kuri’u, 21 na wadanda suka amince da ita 10 na wadanda basu kada kuri’unsu ba sannan 3 na wadanda suka ki amincewa da ita.
Dokar ta bukaci Iran ta fadawa hukumar halin da wadan nan cibiyoytin suke ciki. Wakilan Iran, Rasha da China sun yi allawadai da matsayin da hukumar da dauka, ta kuma bayyana shi a matsayin siyasa ce ta kin JMI, da kuma munafurci.
Na farko Iran tace, ba zata taba amincewa da hukumar IAEA ba, saboda ta dau bangare kuma tana da hannu a kan yakin da Amurka da HKI suka dora wa kasar. Don haka a yanzun ma tana masu aiki ne.