Iran Ta yi Tir Da Daftarin Kudurin Da Amurka Ta Mikawa Hukumar Nukiliya Ta Duniya

Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi mummunan suka kan matakin da Amurka ta dauka na kokarin kare  harin da takai kan kasar iran inda

Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi mummunan suka kan matakin da Amurka ta dauka na kokarin kare  harin da takai kan kasar iran inda ta miki wani kuduri  a taron gwamnonin hukuma kula da makamashin nukiliya ta duniya.

jakadan din din din na kasar Iran a majalisar dinkin duniya a birnin biyanna ya wallafa a shafinsa na X cewa abin dariya ne ga Amurka wadda ta kaddamar da harin kan iran Amma take gabatar da daftarin kuduri ga kwamitin gwamanoni hukumar IAEA kan ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Kudirin ya bukaci iran ta kaddamar da bayanai game da inda sinadarin yuraniyom yake kuma ta bada dama hukumar nukiliya ta duniya damar isa zuwa ga bangaren cibiyar nukiliyarta, kuma ana sa ran za’a mika daftarin kudurin ne a wannan makon ga hukumar ta IAEA

sai dai kafin kudurin ya samu amincewa akwai bukatatar ya samu amincewar mamabobi 35 na kwamitin gwamnonin hukumar nukiliya ta duniya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted