Iran ta yi tir da harin da Kasar Amurka ta kai kan Na’urar Rada da jiragen sama marasa matuki , kuma ta bayyana shi a matsayin keta yarjejeniyar dakatar bude wuta ne da aka kulla a watan Aprilu, kuma ta jaddada matsayinta na hakkin kare kanta, kuma ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa na taka mata burki
Bayani da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fitar ya nuna cewa harin da Amurka ta kai kan na’urar rada da sauran na’urorin sa ido a kudancin yankin sirik da tsibirin Qeshm keta yarjejeniyar da aka kulla ne ta dakatar da bude wuta .
yace ci gaba da keta yarjejeniyar da Amurka ke ci gaba da yi ya kara tabbatar da cewa ba wai tana so ta kara rage tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya ba ne, tana kare jefa yankin ne cikin yanayi mafi muni sakamakon mataken tsokana da take dauka
Daga kare yace kasar iran tana kare yancin kasar ta ne da dukkan karfin da take da shi da kuma muradu da maslahar alummarta , yace yana da kyau kasashe makwabta su kyautata hakkin makwabtaka kada su bari makiya su yi amfani da kasashensu wajen cutar da iran ta hanyar kai mata hari