Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta yi tir da harin ta’addancin ca aka kai kusa da birnin Moscow na kasar Rasha wanda ya ci rayukan mutane da dama.
Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadiyan ya aike da sakon ta’aziyya da jaje zuwa ga shugaban Majalisar tsaron kasar Rasha Nikolai Patrushev da a ciki ya bayyana alhini da tausayawa akan asarar rayuka mai yawa da harin ta’addancin ya haddasa.
Ahamdiyan ya kuma isar da sakon jamhuriyar musulunci ta Iran zuwa ga al’ummar Rasha da gwamnatinta akan abinda ya faru.
A ranar Juma’a da marece ne dai wasu ‘yan ta’adda su ka kai hari akan cibiyar kasuwanci ta “Crocus” dake bayan birnin Moscow tare da bude wuta kan mai uwa da wabi da ya ci rayuka da kuma jikkata mutane 143.