Iran Ta Yi Allah Wadai Kan Hare-Haren Ta’addancin Yahudawan Sahayoniyya Kan Birnin Beirut

Kasar Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayuniyya suka kai kan birnin Beirut Kakakin ma’aikatar harkokin

Kasar Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayuniyya suka kai kan birnin Beirut

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya yi kakkausar suka kan harin da jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya suka kai kan wani ginin zama a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.

Kan’ani ya bayyana cewa: Daukan matakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka yi a yammacin jiya Talata a matsayin cin zarafi ga ‘yancin kai da ‘yancin fadin kasar Lebanon kuma keta dokokin kasa da kasa ne da kuma kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.

Kakakin ma’aikatar diflomasiyyar Iran ya tabbatar da cewa: Wannan mummunan aiki da aikata laifukan da ‘yan ta’addar yahudawan sahayoniyya suka yi a yankin birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon ko shakka babu ba zai iya hana ‘ya’yan al’umma masu kishi da tsayin daka a kasar Lebanon ci gaba da tafarki madaukaki mai daraja na tallafawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta ba da kuma tsayin daka wajen tunkarar zaluncin yahudawan sahayoniyya masu nuna wariyar al’umma ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments