Iran ta sha awashin kai hari kan dakarun ketare da suka kusanci mashigar Hormuz

Sojojin Jamhuriyar Musulinci ta Iran, sun sha alwashin daukar matakin kai hari kan duk wasu dakarun kasashen waje da suka kusanci mashigar ruwa ta Hormuz.

Sojojin Jamhuriyar Musulinci ta Iran, sun sha alwashin daukar matakin kai hari kan duk wasu dakarun kasashen waje da suka kusanci mashigar ruwa ta Hormuz.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump ya ce Rundunar sojin Amurka za ta fara raka jiragen ruwan ƴan kasuwa da za su wuce ta Mashigar Hormuz, a wannan litinin

Rundunar sojin Iran ta ce za ta kai hari kan dakarun Amurka idan har suka kuskura shiga Mashigar ta Hormuz.

Shirin, wanda Mista Trump ya yi wa laƙabi da Project Freedom, zai kunshi dakarun sojin Amurka dubu goma sha biyar, da jiragen ruwan yaƙi masu lalata makamai masu linzami da kuma jiragen saman yaƙi sama da ɗari.

Tun da farko dama, shugaban kwamitin manufofin harkokin waje da tsaron kasa na majalisar dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya yi gargadin cewa za a ɗauki duk wani yunƙurin Amurka na yin katsalandan a harkokin mashigar ruwan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

A nasa bangare Kwamandan Hadikwatar koli ta sojin Iran ya yi gargadin cewa Sojojin Iran za su kai hari ga duk dakarun kasashen waje, musamman daga sojojin Amurka, da ke yunkurin kusanta ko shiga mashigin Hormuz.

A cikin wata sanarwa, Manjo Janar Ali Abdollahi, kwamandan hedikwatar ta Khatam al-Anbiya, ya sake nanata cewa tsaron mashigar Hormuz yana karkashin ikon sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne kawai.

Ya jaddada cewa duk wata hanyar shiga ta mashigin dole ne ya zama tare da hadin guiwar sojojin Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted