Search
Close this search box.

Iran ta sanar da sabon ministan harkokin waje na rikon kwarya

Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Sayyed Ali Khamenei ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar Mohammad Mokhber ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Sayyed Ali Khamenei ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana

cewa, mataimakin shugaban kasar Mohammad Mokhber ne zai zama shugaban kasar na wucin gadi, kamar yadda dokar  kundin tsarin mulkin kasar ta tanada., inda ya yi kira gare shi da shugabannin ma’aikatun shari’a da na majalisar dokoki da su shirya zaben shugaban kasa a cikin lokacin da doka ta kayyade.

Shi kuma shugaban rikon kwarya Mohammad Mokhber, ya sha alwashin bin tafarkin siyasar tsohon shugaban kasar Raisi yayin wani taron gaggawa da ya yi da shugabannin hukumomin shari’a da na majalisar dokoki.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kanaani, ya sanar da cewa mataimakin ministan harkokin wajen kasar Ali Bagheri Kani ne zai ci gaba da kasancewa a matsayin mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran.

Ali Bagheri Kani shi ne maitaimakin ministan harkokin wajen Iran a kan harkokin siyasar kasa da kasa, wanda kuma shi ne ke jagorantar tawagar kasar da ke gudanar da tattaunawa kan shirin Iran na nukiliya tare da manyan kasashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments