Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi watsi da zargin firay ministan kasar Abania Edi Rama wanda ya rubuta a cikin shafinsa na X a ranar talatan da ta gabata yana zargin kasar Iran da ingiza mutanen kasarsa su yi masa tawaye.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana maida martani ga Rama ne a shafinsa na X shima, inda yayi kira ga firay ministan ya saurari kiran mutanensa mai makon ya zargi wani daga waje da rikita masa kasarsa.
Ya ce, mutanenka suna zarginka da saida kasarsu, da cin hanci da rashawa da kuma lalata shugabancin kasar, ka amsa masu ba wani daga waje ba.
Dubban mutanen Albania a cikin yan kwanakin da suka gabata suka fara fitowa kan tituna musamman wadanda suke kaiwa ga fadar Firay minister suna bukatar ya sauka, don shi azzalumi ne, yana kuma saida kasarsu ga wasu attajiran kasashen waje. Don haka suke rayuwa cikin kunchi da wahala.
Abin lura a nan shi ne, kasar Albaniya ce take bawa kungiyar MKO ta munafukai makiya JMI mafaka tun bayan korarsu daga kasar Iraki bayan faduwar gwamnatin Saddam Husain a shekara 2003.
A halin yanzu kasashen yamma suna amfani da wadannan Iraniyawa don aiwatar da ayyukan ta’addanci a ciki da wajen kasar Iran.