Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya.
Ali Larijani ya kara da cewa; Sun kashe al’ummar Falasdinu, sun hana shi abinci da ruwa, yanzu kuma suna son bayyana kawukansu a matsayin masu ceto da Falasdinawa, don haka wannan taron ba komai ba ne sai wasan kwaikwaiyo.
Taron da aka yi a Sherm-Sheikh na Masar an yi shi ne a karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump wanda kasarsa ce ta kasance a gaba wajen bayar da makamai ga HKI a tsawon lokacin yaki.