Iran Ta Kai Wa Haramtacciyar Kasar Isra’ila Hari

A daren jiya ne dai dakarun kare juyin musulunci na Iran su ka fara kai wa arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya hare-haren daukar fansa saboda

A daren jiya ne dai dakarun kare juyin musulunci na Iran su ka fara kai wa arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya hare-haren daukar fansa saboda kai wa birnin Beirut hari.

A wata sanarwar da dakarun kare juyin musulunci su ka fitar, sun bayyana cewa; Sun kai harin ne akan sansanin sojan saman a Haramtacciyar Kasar Isra’ila na “Ramat-David” saboda daukar fansa akan harin da su ka kai wa unguwar Dhahiya a birnin Beirut.

Sanarwar ta kuma ce; “A ranar 8 ga watan Aprilu mun amince da tsagaita wutar yaki ne bisa sharadin cewa za a dakatar da yaki akan dukkanin fagage, amma Amurka da ‘yan sahayoniya, ba su aiki da shi, sun ci gaba da kai hare-hare da tafka laifuka a Lebanon. Haka nan kuma sun rika keta yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare akan kwale-kwalen Iran a mashigar ruwan Hurmuz da tekun Oman da tekun India.”

A karshe sanarwar ta ce, farmakin da aka kai gargadi ne kadai, amma idan aka ci gaba da maimaita keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, to martanin da za a mayar zai zama mai tsanani, zai kuma shafi dukkanin cibiyoyin Amurka da na ‘yan sahayoniya a cikin wannan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted