Hedikwatar Rundunar Sojin Khatam al-Anbiya ta Iran ya bayyana cewa: Rundunar Sojin Iran tana kai hare-hare kan sansanonin Amurka a yankin don mayar da martani ga hare-haren da aka kai wa biranen Iran
Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan hedikwatar rundunar sojin ruwa ta biyar ta Amurka da ke kasar Bahrain da sanyin safiyar Laraba, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da aka kai a wurare da dama a Jask, Sirik, da Qeshm a lardin Hormozgan, kudancin Iran.
Rundunar IRGC ta bayyana cewa: “Rundunar sojin kare juyin juya halin ta kai wani babban hari kan sansanonin Amurka a yankin,”tana mai tabbatar da cewa wannan hari martani ne ga hare-haren da aka kai wa Jask, Sirik, da Qeshm.
Sanarwar ta kara da cewa: “Hare-haren sun kasance masu karfi “tana gargadin cewa duk wani maimaita abin da ta bayyana a matsayin harin Amurka za a kalubalance shi da “hare-haren da suka fi tsanani kan manufar Amurka a yankin.”
Sanarwar ta lura cewa: “Har yanzu ana ci gaba da arangama a kudancin kasar,” yayin da take tabbatar da shirye-shiryen dakarun Iran na mayar da martani ga duk wani karin tashin hankali, tana mai nuni da fadada ayyukan idan hare-haren suka ci gaba.